Mark 1

Yohanna Mai Baftisma Ya Shirya Hanya

1Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā ba su da Ɗan Allah.


2An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, cewa:

“Zan aika ɗan aikina yǎ sha gabanka,
wanda zai shirya hanyarka”
Mal 3.1

3“muryar mai kira a hamada tana cewa,
‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,
ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”
Ish 40.3

4Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma waʼazin baftismar tuba don gafarar zunubai. 5Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun. 6Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, yan kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fari ne da kuma zumar jeji. 7Wannan kuwa shi ne saƙonsa: “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba. 8Ina muku baftisma da
Ko kuwa a cikin
ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

Baftisma da kuma Gwajin Yesu

9A lokacin, Yesu ya zo daga Nazaret na Galili, Yohanna kuwa ya yi masa baftisma a Urdun. 10Da Yesu yana fitowa daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhu kuma yana saukowa a kansa kamar kurciya. 11Sai murya ta fito daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, da kai kuma nake fari ciki ƙwarai.”

12Nan da nan, sai Ruhu ya kai shi cikin hamada, 13ya kuma kasance a hamada kwana arbaʼin, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, malaʼiku kuma suka yi masa hidima.

Kiran Almajirai na Farko

14Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah. 15Yana ce, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”

16Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗanʼuwansa Andarawus, suna jefa taru cikin tafkin, domin su masunta ne. 17Yesu ya ce, “Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.” 18Nan da nan, suka bar tarunansu, suka bi shi.

19Da ya yi gaba kaɗan, sai ya ga Yaƙub ɗan Zebedi, da ɗanʼuwansa Yohanna a cikin jirgin ruwa, suna gyaran tarunansu. 20Ba da ɓata lokaci ba, ya kira su, sai suka bar mahaifinsu Zebedi a cikin jirgin ruwan, tare da ʼyan haya, suka kuwa bi shi.

Yesu Ya Fitar da Mugun Ruhu

21Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majamiʼa ya fara koyarwa. 22Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba. 23Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majamiʼarsu, ya ɗaga murya ya ce, 24“Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai-Mai Tsarki nan na Allah!”

25Yesu ya tsauta masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!” 26Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.

27Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa— kuma da iko! Yana ma ba wan mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.”

28Labari game da shi ya bazu nan da nan koʼina a dukan yankin Galili.

Yesu Ya Warkar da Mutane da Yawa

29Da suka bar majamiʼar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna. 30Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.

32A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu. 33Duk garin ya taru a ƙofar gidan. 34Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.

Yesu Ya Yi Adduʼa a Wurin da ba Kowa

35Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi adduʼa. 36Siman da abokansa suka fita nemansa. 37Da suka same shi, sai suka ce, “Kowa yana nemanka!”

38Yesu ya amsa, ya ce, “Mu je wani wuri dabam-zuwa ƙauyukan da suke kusa-don in yi waʼazi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.” 39Sai ya tafi koʼina a Galili, yana waʼazi a majamiʼunsu, yana kuma fitar da aljanu.

Mutum Mai Kuturta

40Wani mutum mai kuturta
Kalmar Girik da aka yi amfani da ita don kowace irin cutar da ta shafi fatar jiki-ba lalle sai kuturta ba.
ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi, ya ce, “In kana so, za ka iya tsabtace ni.”

41Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin, ya ce, “Na yarda, ka tsabtace!” 42Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke.

43Yesu ya sallame shi nan take, da gargaɗi mai ƙarfi, cewa, 44“Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yǎ zama shaida gare su.” 45A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga koʼina.

Copyright information for HauSRK